Labarai
Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta jagoranci zama na musamman da Shugabannin hukumomin tsaro tare da shugabannin Yan Kasuwar siyar da waya, domin lalubo hanyoyin da za’a bi don magance matsalar kwacen waya a jihar.

Shugaban Hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji ne ya jagoranci zaman a sakatariyar hukumar dake Kan hanyar Abdullahi Bayero.
Sheikh Daneji Wanda ya sami wakikincin Kwamishina na 2, a hukumar Sheikh Ali Danabba ya ce, wannan zama da aka gudanar ya fito da bayanan daya kamata su sani, domin kawo karshen matsalar baki daya.
Sheikh Dan Abba ya kara da cewa akwai bukatar Al’umma su cire tsoro a duk lokacin da irin wannan matasan suka zo domin yin ta’addancin.
A Jawabinsu daban daban , Shugabannin kasuwar sai da waya na Beruit da Farm Center sun yaba da wannan yunkuri na hukumar tare da alkawarin ba da hadin kai domin ganin an kawo karshen wannan matsala a Jahar Kano.




