Ketare

Birtaniya da EU za su yi tattaunawa da Iran yayin da Trump ya sa wa’adin makonni biyu kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa da Jamus za su yi tattaunawa da takwaransu na Iran a Geneva yau a matsayin wani bangare na kokarin kawo karshen rikicin Isra’ila da Iran.

Fadar White House ta ce Donald Trump zai yanke shawara cikin makonni biyu masu zuwa ko Amurka za ta shiga cikin rikicin kai tsaye.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hari kan wuraren soji da dama a Iran a daren jiya – Iran ma ta harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila.

Kimanin makamai 120 aka yi amfani da su wajen kai hare-haren, wanda suka nufi wuraren kera makaman soja da cibiyar binciken nukiliya, wanda sojojin Isra’ila suka ce tana da hannu a ci gaban makaman nukiliyar Iran.

*

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button