Ketare

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce nan da makwanni biyu zai yanke shawara kan ko zai shigar wa Isra’ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka.

A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt ta karanto, Trump ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu.

Waadin yanke shawarar da Trump ya bayar na zuwa ne bayan kwanaki ana rade-radin cewa Amurka za ta shigar wa Isra’ila yaƙin da ta ƙaddamar don ganin ta hana Iran mallakar makaman nukiliya.

Trump dai ya shafe makonni yana bibiyar hanyar diflomasiyya don cimma yarjejeniyar nukiliya da Iran wadda ya soma tattaunawa da ita tun a wa’adinsa na farko a shekarar 2018.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button