Labarai
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kadamar da wasu mahinman aiyuka yau a jahar Kaduna.
Aiyukan dai gwamnan jahar Uba Sani ne ya samar dasu a cikin shekaru biyu da yayi yana mulkin jahar.
Wasu daga cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da: asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya.
Daga nan kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i, da kuma motocin sufuri masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.




