Labarai

Majalisar Wakilai ta kaddamar da fara bincike kan yadda aka bayar da bashin Naira Tiriliyan 1.12 na Shirin Anchor Borrowers

Binciken ya kuma shafi yadda bankin NIRSAL ya raba Naira biliyan 215 ga manoma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) ya ba da Naira biliyan 3 ga kanan manoma da yawansu ya kai dubu 22,120 na shirin Agriculture Value Chain Financing (AVCF).

A lokacin da ake zaman sauraren bayanai kan yadda aikin ya gudana , Shugaban Kwamitin, Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwa kan yadda cibiyoyin hada-hadar kudi 24 suka raba kudaden shirin Anchor Borrowers, wanda ‘yan majalisar suka tabbatar da guda 9 ne kada suka iya gudanar da shirin rabon kudin.

Okafor ya ce daya daga cikin muhimman ayyukan kwamitin majalisar shi ne sanya idanu don tabbatar da yadda hukumomin gwamnati ke aiwatar da shirye-shiryen bayar da tallafi da bunkasa kasa da abinci.

Tun da fari da ya ke jawabi wakilin bankin NIRSAL Charles Bassey, ya cea matsalar rashin tsaro ita ce babbar kalubale na dakile aiwatar da shirin bayar da lamunin da ke karkashin kulawarsu.

A na sa bangaren, Shugaban kula da sashen Kudi, Noma da Ma’adinai na Bankin Sterling, Olushola Obikanye, ya ce bankin ya mayar da Naira biliyan 113 da miliyan 49 zuwa Babban Bankin Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button