Isra’ila da Iran sun yi musayar hare-hare; sabon ‘kisan kiyashi’ a Gaza na masu neman taimako

Fashe-fashe suna cigaba a Tehran kuma makamai masu linzami sun faɗa Tel Aviv yayin da Isra’ila da Iran ke musayar hare-hare masu muni na tsawon kwana biyar a jere.
Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kashe shugaban hafsan sojin Iran a lokacin yaƙi bayan kafofin watsa labarai na Iran sun ce ana shirye-shiryen kai hari mafi girma da kuma mai tsanani na makamai masu linzami a ƙasar Isra’ila.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana neman “ƙarshen gaske” ga rikicin kuma “ba tsagaita wuta ba”, bayan ya fitar da gargadi a kafafen sada zumunta yana kira ga mazauna Tehran su gudu yayin da yake alwashin cewa Iran ba za ta iya samun makamin nukiliya ba.
Firamistan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce kashe Jagoran Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai kara tayar da husuma ba, amma zai “kawo karshen rikicin”.




