Kotun Jamus ta yanke wa likitan Siriya hukunci kan laifukan cin zarafin bil’adama

Wata kotu a Jamus ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wani likita dan kasar Siriya da aka same shi da laifin aikata azabtarwa a matsayin wani bangare na mummunan murkushe ‘yan adawa da Bashar al-Assad ya yi.
Kotun daukaka kara ta Frankfurt ta yanke hukunci kan Alaa Mousa a ranar Litinin, inda ta yanke hukuncin cewa ayyukan likitan sun kasance wani bangare na yakin “mugunta da danniya” na gwamnatin Assad kan ‘yan adawa.
Kotun ta samu dan shekaru 40 da haihuwa da laifukan cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai da azabtarwa, dangane da ayyukan da aka aikata a yakin basasar Syria tsakanin 2011 da 2012.
Shari’ar, wadda ta gudana fiye da shekaru uku, tana daya daga cikin shari’o’in da suka fi muhimmanci da aka kawo karkashin ka’idar ikon shari’a na duniya ta Jamus, wadda ke ba da damar a gurfanar da manyan laifuka da aka aikata a kasashen waje a cikin gida.



