Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Bukatar ICPC Ta Tsare El-Rufai Na Karin Kwanaki 14

Wata kotun majistare da ke Abuja ta sanya ranar Talata, 17 ga Maris domin yanke hukunci kan sabuwar bukatar Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) na neman karin kwanaki 14 domin ci gaba da tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Majistare Okechukwu Akweke ne ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar domin tantance ko za a amince da bukatar hukumar ko kuma a’a.
Ana tsare Nasir El-Rufai tun ranar 18 ga Fabrairu 2026 bisa zargin badakalar kudade da kuma saurarar bayanan sirri na mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Tun da farko dai ICPC ta samu umarnin kotu na tsare shi na kwanaki 14 daga wata kotun majistare da ke Bwari a ranar 19 ga Fabrairu, amma wa’adin umarnin ya kare ne a ranar 5 ga Maris.
Sai dai lauyoyin Nasir El-Rufai da magoya bayansa sun soki ci gaba da tsare shi bayan karewar wa’adin kotu, suna mai cewa hakan ya sabawa doka.




