An kama ‘dan bindiga Sule Yellow bayan bidiyon sa na garkuwa da mutane ya bazu a TikTok

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargi da kasancewa ɗan bindiga, Sule Yellow, wanda ya shahara a kafar TikTok bayan wani bidiyo na kai tsaye (livestream) da ya nuna ana zargin yana nuna ayyukan garkuwa da mutane da kudin fansa.
Bidiyon wanda ya bazu a ranar 4 ga Maris ya nuna Sule Yellow tare da wani da ake kira Auta da wasu mambobin ƙungiyarsu, inda ake zargin sun yi taƙama da ayyukan satar mutane.
A wani bidiyo da ke yawo a kafar X, an ga Sule Yellow an ɗaure masa hannu da ankwa yayin da sojoji ke masa tambayoyi kan makaman da ake zargin na ƙungiyarsa ne.
Bidiyon ya kuma nuna jami’an tsaro suna nuna wata leda da ake zargin ta ƙunshi kuɗin fansa da aka ƙwato daga wani satar mutane da ake dangantawa da ƙungiyar.
Har yanzu hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan yadda aka kama shi ba.
Kamen nasa na zuwa ne yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da hare-hare kan ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke kai hare-hare tare da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.



