Gwamnan Kano Ya Rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Ya Haɗa Ta da Ma’aikatar Ilimi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi tare da haɗa ta da Ma’aikatar Ilimi domin ƙarfafa daidaito da kuma hanzarta sauye-sauye a fannin ilimi a jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
Kafin wannan sauyi, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, shi ne ke jagorantar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi a matsayin kwamishina.
Sanarwar ta bayyana cewa bayan wannan sauyi, sabuwar ma’aikatar za ta ci gaba da aiki da sunan Ma’aikatar Ilimi, inda za a ƙirƙiri wani sashen kula da ilimi mai zurfi (Directorate of Higher Education) a cikinta domin kula da harkokin jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi na jihar.
Za a naɗa Babban Sakatare (Permanent Secretary) domin jagorantar sashen tare da samar da ma’aikatan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen gudanar da harkokin manyan makarantun gaba da sakandare.
Haka kuma, dukkan hukumomin da ke ƙarƙashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, ciki har da Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano (Scholarship Board), za su koma ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi.
Jami’o’in da gwamnatin jihar ke da su da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi ma za su kasance ƙarƙashin kulawar sabon sashen da aka kafa.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na shirin gyaran tsarin ilimi da take aiwatarwa domin sake farfaɗo da fannin, kawar da maimaita ayyuka tsakanin ma’aikatu, inganta daidaiton manufofi a dukkan matakan ilimi, da kuma rage kuɗin tafiyar da gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa an dauki wannan mataki ne domin rage tsadar gudanar da gwamnati tare da ƙara inganci da gaskiya a tafiyar da harkokin ilimi a jihar.
A ƙarshe, gwamnan ya umarci Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati su tabbatar da aiwatar da wannan sauyi cikin gaggawa a dukkan ma’aikatun da abin ya shafa.




