Matashin ɗan jarida Rabi’u Sani Hassan da aka fi sani da Yaron Kirki ya ajiye aikin da tashar Hikima Radio Kano

Arewa Updates ta rawaito cewa, Rabi’u Sani Hassan Yaron Kirki ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Jumuʼa 13 ga Maris 2026.
Sanarwar ta ce ya dauki matakin ajiye aikin ne domin samun damar mayar da hankali kan harkokin ilimi da suka hada da karatu da koyarwa a fannin aikin jarida.
Ya kuma gode wa shugabannin Hikima Radio na baya da na yanzu tare da daukacin ma’aikatan gidan rediyon bisa hadin kai da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake aiki da su.
Sanarwar ta kuma nuna godiya ga abokan aiki da abokan hulda da ya ce sun ba shi goyon baya a tsawon lokacin aikinsa a gidan rediyon.
Yaron Kirki ya yi aiki da tashar Aminci Radio, Jalla Radio, Tambari TV kafin Hikima Radio.
Ya ƙware a gabatar da shirye-shirye da jagorantar zangon shirye-shirye, labarai da rahotonni da alʼamuran kafafen sada zumunta.
Wasu maʼaikatan Hikima sun nuna alhinin rabuwa da shi, a daidai lokacin da suka ce ana tsananin buƙatar ayyukansa.
Wannan dai na zuwa ne yayin da guguwar barin aiki ke ci gaba da ci kamar wutar daji a tashar.



