Labarai

Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gyaran Bangaren Man Fetur a Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin musamman domin tsara sabon matakin gyare-gyare a bangaren man fetur na Nigeria.

 

 

Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana cewa an kafa Kwamitin Presidential Petroleum Reform & Value Optimisation Taskforce ne domin tsara hanyoyin inganta tsarin harkar man fetur da kuma ƙara darajar albarkatun makamashi na ƙasar.

 

 

An naɗa shahararren ɗan kasuwa kuma wanda ya kafa bankin Guaranty Trust Bank, Fola Adeola, a matsayin shugaban kwamitin, wanda zai jagoranci aikin tare da tabbatar da kammala aikinsa cikin lokaci.

 

 

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Ademola Adeyemi-Bero, Osagie Okunbor, Abubakar Suleiman, Adaeze Aguele, Farouk Gumel, Phillipa Osakwe-Okoye da Seyi Bella, yayin da Mofoluwasho Fadayomi zai kasance sakataren kwamitin.

 

 

Kwamitin zai yi aiki na wucin gadi domin tsara manufofin da za su ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi a bangaren man fetur, da kuma jawo sabbin jarin da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

 

 

Rahoton ya ce kwamitin zai gabatar da rahoton wucin gadi bayan watanni uku, sannan ya mika cikakken rahotonsa cikin watanni shida bayan kaddamar da shi.

 

 

A cikin aikinsa, ana sa ran kwamitin zai gabatar da manyan tsare-tsare guda uku, ciki har da hanyoyin gyaran tsarin harkar man fetur cikin gaggawa, shirin jawo jarin dala biliyan 5 zuwa 10 a bangaren, da kuma dabarar sauya tsarin makamashi na ƙasa na tsawon shekaru goma.

Shugaban ƙasa ya kuma umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati da su bai wa kwamitin cikakken goyon baya tare da daidaita ayyukansu da sabon tsarin gyaran bangaren man fetur.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button