Siyasa

Rigima Ta Barke Tsakanin Kansiloli da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kano Municipal Kan Rabon Shinkafar Azumi

Wasu kansiloli a Ƙaramar Hukumar Kano Municipal sun nuna rashin jin daɗi kan yadda aka gudanar da rabon shinkafar azumi ga al’umma.

Rahotanni sun bayyana cewa ce-ce-ku-cen ya fara ne bayan wani labari da ya yaɗu a kafafen sada zumunta cewa shugaban ƙaramar hukumar, Malam Saleem Hashim, ya bai wa kansiloli buhunan shinkafa kusan 80 domin su raba wa al’ummar yankunansu.

Sai dai wasu kansilolin sun musanta hakan, inda suka fara wallafa saƙonni a shafukansu na Facebook suna nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da rabon.

Kansilan Mazabar Yakasai, Hon. Ahmad Na’annabi, shi ne ya fi bayyana ra’ayinsa kan lamarin.

Ya zargi shugaban ƙaramar hukumar da rashin nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC lamarin da ya ce yana kawo cikas ga ayyukan siyasa a yankin.

Na’annabi ya kuma yi zargin cewa shugaban ƙaramar hukumar yana binsa bashin naira 659,000 fiye da watanni takwas ba tare da biyan sa ba.

Haka kuma ya koka cewa kansiloli na fuskantar matsin lamba daga jama’ar mazabunsu, saboda suna zarginsu da rashin taimako alhali ba sa samun isasshen tallafi daga ƙaramar hukuma.

Ya ƙara da cewa tirela guda ɗaya na shinkafa mai ɗauke da buhu 600 da aka ce gwamnan jihar ya bayar, kansiloli sun samu buhu guda ɗaya kacal kowannensu, inda ya bukaci a bayyana yadda aka raba sauran buhunan.

Bugu da ƙari, kansilan ya zargi cewa ba a shawarci kansiloli ba wajen rabon mukamai a ƙaramar hukumar, tare da cewa ba a ba su damar gabatar da sunayen mutanen da za a naɗa ba.

A wani mataki, ya ɗora hoton mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Malam Jamilu Salisu Sharfaɗi, tare da barazanar cewa za su kai batun majalisa domin fara shirin tsige shugaban ƙaramar hukumar.

 

Arewa Updates

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button