Siyasa

Tambuwal ya koma jam’iyyar ADC bayan ficewa daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanatan da ke wakiltar mazaɓar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa ta Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal, ya sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC bayan ficewar daga Jam’iyyar PDP.

 

Tsohon gwamnan ya sanar da sauya sheƙr nasa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce matakin da ya ɗauka na komawa ADC ya samo asali ne daga ra’ayinsa cewa Najeriya na buƙatar wani ƙarfi na siyasa da ya ginu kan gaskiya da haɗin kai da riƙon amana da kuma jajircewa wajen bunƙasa ƙasar.

 

Ya kuma sake jaddada ƙudurinsa na ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da tsayawa kan manufofin dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa.

 

Tun da farko dai Tambuwal ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da saɓanin shugabanci da kuma rabuwar kai da ke ƙara ƙamari a cikin jam’iyyar.

 

A cewarsa,”rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyar PDP sun raunana haɗin kai da alƙiblar da a baya suka kasance ginshiƙan jam’iyyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button