NNPP Ta Zargi An Tura Sama da Naira Miliyan 500 Zuwa Asusun Muhuyi Magaji Rimin Gado ba bisa ka’ida ba

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta yi zargin cewa an tura sama da naira miliyan 500 daga asusun kananan hukumomi 44 na jihar zuwa asusun bankin tsohon shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Kakakin jam’iyyar a Kano, Engr. Ibrahim Karaye, ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa, inda ya ce an tura kudin ne a shekarar 2024 zuwa wani asusun Zenith Bank da ya kare da lamba 140.
Karaye ya ce an raba kudin ne daga kowace karamar hukuma a jihar, inda aka bayyana shi a matsayin kudin shari’a, sai dai ya ce har yanzu ba a fayyace takamaiman shari’ar da kudin ya shafa ba.
Ya kara da cewa abin mamaki ne yadda mutumin da ake magana a kansa ke zargin wasu da satar dukiyar al’umma, duk da cewa akwai wasu bayanai da ke nuna akasin hakan.
A cewarsa, jam’iyyar na da wasu bayanai da suka shafi wasu ayyuka da aka gudanar a shirin tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin Kano ta hannunsa.
Har ila yau, Karaye ya yi ikirarin cewa an taba kai wasu kudade zuwa kasar Sudan domin biyan kudin makarantar wasu dalibai duk da cewa akwai hukumomin gwamnati da ke da alhakin irin wannan aiki.
Ya kara da cewa idan jam’iyyar ta fara fitar da wasu takardu da hujjojin da take da su, wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a gwamnati ba za su iya fita bainar jama’a ba saboda kunya.
A karshe, ya kalubalanci Muhuyi Magaji Rimin Gado da ya bayyana hukuncin da dokar Najeriya ta tanada kan zargin aikata laifin wanke kudade (money laundering).




