Ketare
Mutum 64 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa a kudancin Habasha

Rahotanni daga hukumomin yankin kudancin Habasha sun bayyana cewa ambaliyar ruwa dazaftarewar ƙasa sakamakon ruwan sama mai ƙarfi sun kashe mutum 64, yayin da ba a san inda mutum 95 suke ba.
Shugaban ƴansanda a yankin Gamo, Abraham Buha, ya bayyana cewa an samu mutuwar mutanen ne a ƙananan hukumomin Kamba, Gacho Baba, da Bonke na Gamo.
A baya dai, gwamnatin Gamo ta bayyana cewa mutum 52 ne kawai suka mutu a yankin Mazo Deysa na ƙaramar hukumar Gacho Baba.
Jami’an gwamnatin tarayya da na yankin sun kai ziyara ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, yayin da ayyukan ceto da bincike ke ci gaba




