Kotu Ta Ba ICPC Damar Ci Gaba da Tsare El-Rufai Na Kwanaki 14

Wata kotu ta ba Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC damar ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, na tsawon ƙarin kwanaki 14 domin kammala bincike kan zarge-zargen da ake masa.
Rahotanni sun ce kotun ta bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis bayan hukumar ta gabatar da buƙatar samun ƙarin lokaci domin zurfafa bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma wasu laifuffuka da ake zargin tsohon gwamnan da su.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ICPC ta bayyana cewa ƙarin lokacin zai ba ta damar tattara bayanai da kammala binciken da ake yi kan batun.
An ce an bayar da umarnin ne a gaban lauyan El-Rufai, kuma wa’adin tsarewar zai ƙare ne a ranar 19 ga watan Maris.
Sai dai lauyan tsohon gwamnan ya garzaya Babbar Kotun Majistare da ke Bwari a Abuja, inda ya shigar da ƙara yana neman a soke umarnin tsarewar, yana mai cewa ba a bi ƙa’idojin doka yadda ya kamata ba wajen tsare El-Rufai.
Duk da haka, kotun ta bayyana cewa akwai buƙatar a ci gaba da tsare tsohon gwamnan har sai an kammala binciken da ake yi a kansa.
A halin yanzu, Babban Mai Shari’a na kotun, Okechukwu John Akweke, ya sanya ranar 17 ga watan Maris domin yanke hukunci kan ko za a soke wannan sabon umarnin tsarewar ko a’a.




