Harin ’Yan Daba Ya Yi Sanadin Mutuwar Ɗan Kwamitin Tsaro a Kano

Al’ummar unguwar Tukuntawa da ke jihar Kano sun shiga alhini bayan da wasu ’yan daba suka kashe wani matashi dan kwamitin tsaron yankin mai suna Usaini Bashir Sabo.
Jaridar Arewa Updates ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Maris, 2026, inda aka ce matashin ya gamu da ajalinsa sakamakon mummunan harin da ’yan daban suka kai masa.
A cikin wata sanarwa da Auwal Soja ya fitar a madadin kwamitin tsaron yankin Tukuntawa, ya bayyana cewa marigayin na daga cikin matasan da ke taimakawa wajen kula da tsaron al’umma domin dakile ayyukan bata-gari a unguwar.
Sanarwar ta ce ’yan daban sun kai wa matashin hari inda suka yi masa sara a tsakiyar kai, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa.
Biyo bayan faruwar lamarin, Majalisar Matasa ta Kasa reshen jihar Kano ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakan da suka dace domin magance matsalar ’yan daba a yankin.
A wata sanarwa da Shugaban majalisar a jihar Kano, Hassan Garba Abdullahi, ya aikawa Arewa Updates, ya nuna matukar damuwa kan kisan gillar, yana mai cewa lamarin ya kara nuna bukatar kara daukar tsauraran matakai kan matsalar daba a jihar.
Majalisar ta kuma ba da shawarar kafa ofishin ’yan sanda a unguwar Tukuntawa, musamman a bayan gidan namun dajin Kano (Gidan Zoo), domin kara karfafa tsaro da kuma dakile ayyukan ’yan daba a yankin.
Ta kuma bukaci hukumomi da al’umma su hada kai wajen nemo mafita domin kawo karshen matsalar daba da ke addabar wasu sassan jihar Kano.




