Lauyoyin gwamnatin Kano za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyar Lauyoyin gwamnati ta Najeriya reshen jihar Kano (LOAN) ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga tsakar daren ranar Talata 11 ga Maris, 2026, sakamakon matsalolin da ta ce gwamnatin jihar ta gaza warwarewa.
Shugaban kungiyar a Kano, Barista Aminu Abdullahi Shams, ya bayyana wa manema labarai cewa sun dauki matakin ne bayan shekaru na koke-koke da tattaunawa da gwamnati ba tare da samun mafita ba.
Ya ce duk da kafa kwamitoci da kuma wasu alkawurran da gwamnati ta yi, har yanzu ba a aiwatar da su ba, lamarin da ya tilasta musu komawa yajin aiki bayan sun dakatar da wani da suka shirya a watan Fabrairu.
Kungiyar ta ce daga cikin matsalolin da suke kokawa da su akwai rashin biyan albashi da alawus yadda ya kamata kamar yadda ake yi wa takwarorinsu a jihar Jigawa, rashin biyan wasu alawus-alawus tun 2017, da kuma bashin albashin watanni biyu na sabbin lauyoyin gwamnati.
Sauran koke-koken sun hada da rashin kayayyakin ofisoshi, rashin motocin aiki ga lauyoyin gwamnati, da kuma rashin biyan alawus din man fetur na Naira 170,000 da ake bai wa alkalai tun daga Janairu 2024.
Kungiyar ta ce dukkan jami’an lauyoyi na gwamnati a Kano za su janye aikinsu har sai an biya musu bukatunsu, matakin da ake ganin zai kawo tsaiko ga harkokin shari’a da wakilcin gwamnati a kotuna a jihar.




