Iran tayi barazanar kawar da Donald Trump daga doran Duniya

Wani babban jami’in tsaron ƙasar Iran, Ali Larijani, ya yi gargaɗi ga shugaban Amurka, Donald Trump, inda ya ce ya kamata ya yi hankali domin kada a kai ga “kawar da shi daga duniya”.
Larijani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Iran ba ta tsoron abin da ya kira barazanar Trump mara amfani.
A cewarsa, “Ko waɗanda suka fi ka ƙarfi ba su iya kawar da al’ummar Iran ba,” yana mai ƙara da cewa ya kamata Trump ya yi taka-tsantsan domin kada a kai ga kawar da shi daga duniya.
Kalaman na Larijani sun zo ne bayan Trump ya yi barazana a dandalinsa na Truth Social cewa Amurka za ta ƙara tsaurara hare-harenta kan Iran idan ba ta buɗe mashigar Strait of Hormuz ba, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen safarar man fetur a duniya.



