Labarai
Gwamnan Kano Ya Sauke Shugaban Ma’aikatan Jihar Abdullahi Musa

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Jihar, Alhaji Abdullahi Musa, daga mukaminsa.
Sanarwar sauke shi daga mukamin ta fito ne ta bakin Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, gwamnan ya umarci Babbar Sakatariya Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, da ta ci gaba da rike mukamin Shugaban Ma’aikatan Jihar na rikon kwarya.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sa aka sauke Abdullahi Musa daga mukaminsa ba.




