Labarai
’Yan Bindiga Sun Sace Mutane Biyu a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban Ƙungiyar Matasan Pambegua, Rufai A. Bature, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwar jaje da ya fitar ga al’ummar garin Zuntu bayan harin.
A cikin sanarwar, ya bayyana cewa satar mutanen ta haddasa damuwa a tsakanin mazauna yankin, inda ƙungiyar ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da dukkan al’ummar garin.
Haka kuma, ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya kare al’umma daga irin waɗannan hare-hare, tare da bai wa jami’an tsaro nasarar gano waɗanda suka aikata laifin da kuma ceto waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.
Sanarwar ta kuma buƙaci hukumomin tsaro da shugabannin yankin da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.




