Labarai

’Yan Bindiga Sun Kashe Abdulmalik Isah, Sun Yi Garkuwa da Hajiya Yaya a Makarfi

Majiyoyi daga cikin al’ummar yankin sun tabbatar da cewa harin ya yi sanadin rasuwar Abdulmalik Isah a yayin da aka sace Hajiya Yaya zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Bayan aukuwar lamarin, masallacin Izala da ke Makarfi ya sanar da dakatar da Sallar Tahajjud da aka shirya fara gudanarwa a daren Litinin.

A wata sanarwa da Mataimakin Jami’in Yaɗa Labarai na Izala a Makarfi, Malam Sani Adamu ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon rashin kwanciyar hankali a garin bayan shigowar masu garkuwa da mutane.

Sanarwar ta buƙaci al’umma da su gudanar da Sallar Tahajjud a gidajensu domin kare lafiyarsu, tare da bayyana cewa ana sa ran za a ci gaba da sallar a daren Talata idan al’amura sun daidaita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button