Labarai

Gobara Ta Tashi a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe a Sashen C na ginin, inda wasu sassa na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya suke.

A sakamakon lamarin, an ga wasu ma’aikata suna barin ofisoshin da ke kusa da wurin domin kare lafiyarsu, yayin da aka sanar da jami’an agajin gaggawa domin su kai ɗauki.

Rahoton ya ce jami’an ceto sun yi gaggawar isa wurin domin shawo kan gobarar da kuma hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan ginin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button