Ramadan: Gwamna Abba Ya Ƙaddamar da Raba Buhunan Shinkafa 100,000 na Gidauniyar Dangote a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa 100,000 da Aliko Dangote Foundation ta bayar domin tallafa wa marasa ƙarfi a fadin jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da an raba tallafin cikin gaskiya da adalci, ta hanyar shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ya kai ga mutanen da aka tanada wa.
A nasa bangaren, kwamishinan noma da albarkatun ƙasa na jihar, Dakta Danjuma Mahmud, ya yaba wa gidauniyar Dangote bisa ba gwamnatin jihar damar jagorantar rabon tallafin kai tsaye, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da an raba kayayyakin ga waɗanda suka fi buƙata.
Ya ƙara da cewa wannan tallafi zai taimaka wajen rage raɗaɗin rayuwa ga al’umma musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan.




