Gwamnan Kano Ya Bukaci ’Yan Jarida Su Ƙara Wayar da Kai Kan Manufofin Kano First

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ’yan jarida da masu gudanar da kafafen yaɗa labarai su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma kan manufar Kano First da gwamnatin jihar ta ƙaddamar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin liyafar buɗe baki (Iftar) da gwamnatin jihar ta shirya wa ’yan jarida da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai a Fadar Gwamnati da ke Kano.
Da yake wakiltar gwamnan, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Sulaiman Sani Wali, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da aiki kafada da kafada da kafafen yaɗa labarai domin tallata manufofi da shirye-shiryen da za su kawo ci gaban jihar.
Ya kuma yi alƙawarin isar da bukatu da ƙorafe-ƙorafen da ƙungiyoyin ’yan jarida suka gabatar a wajen taron ga gwamnan domin ɗaukar matakan da suka dace.
A nasa jawabin, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yaba wa rawar da ’yan jarida ke takawa wajen inganta shugabanci nagari da ci gaban jihar Kano.
Sai dai ya yi gargadi kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen tayar da husuma, cin mutunci ko barazana ga jami’an gwamnati, yana mai jaddada buƙatar bin ƙa’idojin ƙwararru a aikin jarida.
shugaban Kano Online Media Forum, Abubakar Abdulkadir Dangambo, da shugaban ƙungiyar ma’aikatan rediyo, talabijin da fasaha ta Najeriya, Radio, Television, Theatre and Arts Workers Union of Nigeria a Kano, Babangida Mamuda Biyamusu.
Dukkansu sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da haɗa kai da gwamnatin jihar Kano domin tallata ci gaba tare da kiyaye ƙa’idoji da ɗa’ar aikin jarida.




