Labarai

Sojoji Sun Kashe Ƴanbindiga 45 Bayan Harin Ramuwar Gayya a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, kamar yadda hukumomin jihar suka tabbatar.

Tun da farko dai ƴanbindigar, waɗanda ake zargin sun taso daga jihar Zamfara sun kai hari ƙauyen Alhazawa da ke ƙaramar hukumar Danmusa a ranar Alhamis domin satar shanu.

Sai dai mazauna ƙauyen sun nuna turjiya ga maharan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar huɗu daga cikin ƴanbindigar.

Bayan kwana guda da faruwar hakan, rahotanni sun ce ƴanbindigar sun sake taruwa domin kai harin ramuwar gayya kan mazauna ƙauyen.

A kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen ne suka yi karo da sojoji, inda aka gwabza musayar wuta mai tsanani.

Majiyoyi sun ce a sakamakon gumurzun ne sojojin suka kashe ƴanbindiga 45, yayin da sojoji uku suka rasa rayukansu a yayin artabun.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button