Labarai

Kotu ta tisa keyar wanda ake zargi da garkuwa da mutane gidan yari

Kotun Majistiri da ke Nomansland, Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali ta soma sauraron shari’ar wani matashi mai suna Sagiru Isa kan zargin garkuwa da ɗan ’yar uwarsa a garin Dungurawa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa

Rahotanni sun ce ana zargin matashin da sace ƙaramin yaro mai suna Sultan Isa, inda ya nemi kudin fansa har naira miliyan biyu daga hannun mahaifin yaron.

 

Daga bisani kuma ana zarginsa da kashe yaron tare da binne shi a wani wuri da ke Kofar Waika, Kano.

Mai gabatar da ƙara, Farida Wada, ta karanta tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda ake zargin a gaban kotu, bayan haka kotun ta aike da shi gidan yari domin jiran shawarar Ma’aikatar Shari’a.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da shari’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button