Kano: Gwamnati Ta Yi Watsi Da Cibiyar Aliko Dangote Saboda Ziyarar da Kwankwaso ya kai — Alkasim Wudil

Tsohon Shugaban Cibiyar Horar da Sana’o’i ta Aliko Dangote (Aliko Dangote Ultra-Modern Skills Acquisition Center) da ke Kano, *Hon. Alkasim Hussaini Wudil* ya yi wasu zarge-zarge masu nauyi game da dalilin da ya sa Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da cibiyar.
A cewar Hon. Wudil, babban dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta janye jiki daga kula da cibiyar shi ne ziyarar da jagoran jam’iyyar NNPP, *Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso* ya kai cibiyar a baya.
Hon. Alkasim ya bayyana cewa Kwankwaso ya kai ziyarar ne domin duba yadda ake gudanar da ayyuka a cibiyar tare da ƙarfafa wa ma’aikata da ɗalibai gwiwa.
Sai dai ya yi zargin cewa wannan ziyara ta zo ne a daidai lokacin da aka soma kiraye-kirayen “Abba Tsaya da Kafarka,” wanda hakan ya sa gwamnatin jihar kallon ziyarar a matsayin wani abu daban.
Watsi Da Cibiyar
Tsohon shugaban ya nuna damuwarsa kan yadda aka bar cibiyar ba tare da kulawar da ta dace ba, yana mai cewa hakan ya faru ne sakamakon rashin jin daɗin ziyarar da aka kai ɗin daga ɓangaren mahukunta.
Ya jaddada cewa cibiyar tana da muhimmanci ƙwarai wajen samar wa matasa ayyukan yi da dogaro da kai, don haka bai kamata siyasa ta shafi ayyukanta ba.
A halin yanzu, gwamnatin jihar ba ta riga ta mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge na Hon. Alkasim Hussaini Wudil ba.
Ahrasjo News




