Ketare

Trump: Ina So In Kasance Cikin Masu Zaɓen Sabon Jagoran Addinin Iran

shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya kamata ya kasance cikin waɗanda za su zaɓi sabon jagoran addinin ƙasar Iran.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Axios, inda ya ce yana kyautata zaton cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran na iya zaɓar ɗan marigayi Ali Khamenei, wato Mojtaba Khamenei, a matsayin sabon jagora.

Sai dai Trump ya ce wannan lamari ne da ba zai amince da shi ba.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Assembly of Experts, wadda ita ce ke da alhakin zaɓen sabon jagoran addinin Iran, ba ta sanar da wanda zai gaji marigayi Ayatollah Ali Khamenei ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button