Labarai

Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zarge-zargen aikata manyan laifuka da suka haɗa da rashin da’a, cin zarafin mukami da kuma karya amana.

 

An bayyana hakan ne bayan da ’yan majalisar suka sanya hannu kan wata takardar sanarwa da aka gabatar a zaman majalisa domin fara aiwatar da matakin tsige shi, bisa tanadin Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).

A cewar ’yan majalisar, matakin ya samo asali ne daga zarge-zargen da suka shafi yadda mataimakin gwamnan ya gudanar da aikinsa tun daga lokacin da yake Kwamishinan Kananan Hukumomi har zuwa lokacin da ya zama mataimakin gwamna.

Takardar tuhumar ta nuna cewa ana zargin Aminu Abdussalam Gwarzo da karɓar kuɗaɗen alfarma daga kananan hukumomi 44 na jihar tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Janairun 2024.

Rahoton ya ce ana zargin yana karɓar kimanin naira miliyan 1.5 duk wata daga kowace ƙaramar hukuma, wanda ya kai kusan naira miliyan 66 a kowane wata, da kuma jimillar kusan naira miliyan 462 cikin watanni bakwai.

Haka kuma, daga watan Fabrairu zuwa Yulin 2024, ana zargin ya sake karɓar wasu ƙarin kuɗaɗe da suka kai naira miliyan 726 da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman ga kananan hukumomin.

Bugu da ƙari, ’yan majalisar sun kuma zarge shi da amfani da mukaminsa wajen sauƙaƙa fitar da naira miliyan 440 daga asusun kananan hukumomi 44 zuwa kamfanin Novomed Pharmaceuticals Limited, abin da suka ce ya saɓa wa dokokin saye da kashe kuɗaɗen gwamnati na jihar.

Majalisar ta bayyana cewa dukkan waɗannan zarge-zarge sun kai matsayin manyan laifuka na rashin da’a kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, don haka ta fara matakan doka domin tsige mataimakin gwamnan daga mukaminsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button