Uncategorized

Kotu Ta Wanke DCP Abba Kyari Daga Zargin Boye Kadarori

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta wanke tare da sallamar dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, DCP Abba Kyari, daga tuhume-tuhume guda 23 da suka shafi zargin kin bayyana kadarori.

Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta gaza gabatar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da zargin da ake yi wa Kyari.

NDLEA ta shigar da karar ne tare da tuhumar Kyari da wasu ‘yan’uwansa biyu da rantsuwar ƙarya domin boye asalin wasu kadarori da ake zargin suna da alaka da shi.

Sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara ba su kawo hujjoji ko takardun da ke tabbatar da cewa wasu filaye da ke Fountain Estate, Kasana mallakin Kyari ba ne, ko kuma hujjojin da za su danganta shi da wasu kadarori da ke Asokoro a Abuja da kuma Maiduguri a Jihar Borno.

 

A bangaren kariyarsa, Abba Kyari ya shaida wa kotu cewa kadarorin da ke Borno mallakin mahaifinsa ne, wanda ya gada tare da ‘yan’uwansa, kuma masu gabatar da kara ba su iya karyata wannan bayani ba.

 

Bisa haka, kotun ta yanke hukuncin sallamar su baki daya daga zargin da ake musu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button