Amurka Ta Zargi Iran Da Yunkurin Kashe Donald Trump

Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa Iran ta yi yunkurin kashe shugaban kasar Amurka, Donald Trump, inda ta kara da cewa sojojin Amurka sun kashe wani jami’in Iran da ake zargi da jagorantar shirin.
Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar ma’aikatar tsaron Amurka ta The Pentagon.
A cewarsa, Iran ta yi yunkurin kashe Trump, amma daga karshe shirin bai yi nasara ba.
Tun a shekarar 2024 ma gwamnatin Amurka ta gurfanar da wani dan asalin Afghanistan a gaban kuliya bisa zargin hannu a wani shiri da ake zargin Iran ta shirya domin kashe Trump kafin ya fara aiki bayan nasararsa a zaben waccan shekarar.
Tsohon babban lauyan gwamnatin Amurka, Merrick Garland, ya kuma bayyana cewa ma’aikatar shari’a ta tuhumi wani mutum da ake zargi yana aiki da gwamnatin Iran, wanda ake zargin shi ne ya jagoranci wasu masu aikata laifi domin aiwatar da shirin kashe wasu mutane ciki har da Trump.
Sai dai gwamnatin Iran ta musanta zarge-zargen, inda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ya ce ba wannan ne karon farko da ake yi wa Iran irin wannan zargi ba, yana mai cewa a baya ma an yi zarge-zargen makamantan haka amma daga baya aka gano ba gaskiya ba ne.




