Labarai

Ƴansanda sun kama wanda ake zargi da yaɗa saƙon tunzuri a Kano

Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da yaɗa saƙonnin bidiyo da murya masu tayar da hankali da ka iya haddasa rikici da firgita mazauna jihar.

 

A wata sanarwa da kwamishinan ’yansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya fitar a ranar 5 ga Maris, 2026, ya bayyana cewa rundunar ta gano yadda ake yaɗa saƙonnin a kafafen sada zumunta, inda ake zargin suna ɗauke da kalamai masu tunzura jama’a da ka iya haddasa rashin zaman lafiya.

 

Sanarwar ta ce rundunar ta gudanar da wani samame na musamman inda ta samu nasarar kama wanda ake zargin, kuma a halin yanzu ana yi masa tambayoyi domin ci gaba da bincike.

 

Rundunar ta jaddada cewa tana ɗaukar irin waɗannan kalamai masu tunzura jama’a da matuƙar muhimmanci, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

’Yansandan sun kuma yi Allah-wadai da ƙirƙira da yaɗa irin waɗannan saƙonni, tare da gargadin duk wanda ke da hannu a ciki da ya daina nan take. Rundunar ta ce duk wanda aka kama yana yaɗa bayanan ƙarya ko kalaman ƙiyayya za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban doka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button