NNPP Ta Bankado Zargin Siyar da Motocin Gwamnatin Kano ga Muhyi Magaji Kan Farashi Mai Rahusa

Zargin ya fito ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan matakin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na kwato motocin gwamnati daga hannun wasu kwamishinoni da suka yi murabus, bayan da suka bi sahun Rabiu Musa Kwankwaso.
Mai magana da yawun NNPP na riko a jihar Kano, Ibrahim Karaye, shi ne ya wallafa takardar cinikin a shafinsa na Facebook, wacce jaridar Daily Nigerian Hausa ta tabbatar da gani.
A cewar takardar mai ɗauke da kwanan watan 19/08/2025, an nuna cewa gwamnatin ta siyar wa Muhyi mota kirar Toyota Corolla kan kuɗi Naira 425,000 kacal.
Haka kuma, an siyar masa da mota kirar Nissan Hilux kan Naira 833,333.33.
Jimillar kuɗin motocin biyu ya kai Naira 1,258,333.33, lamarin da ya janyo muhawara a tsakanin al’umma, musamman duba da darajar irin waɗannan motoci a kasuwa.




