Labarai

Takaddama Ta Ƙara Ƙamari a Unguwa Uku GSM Market Kan Batun Zaɓen Shugabanni

Wasu daga cikin ’yan kasuwar sayar da wayoyin hannu da na’urorinsu a Unguwa Uku GSM Market sun koka kan abin da suka kira mulkin kama-karya da kuma cin zarafi daga shugabancin kasuwar.

Matasan sun bayyana cewa sun daɗe suna buƙatar a gudanar da ingantaccen zaɓe domin zaɓen sabbin shugabanni, amma sun zargi cewa shugaban kasuwar yana hana gudanar da zaɓen. Sun kuma yi iƙirarin cewa ana gallaza musu tare da haɗa kai da wani tsohon jami’in ɗan sanda, lamarin da suka ce ya kai ga gurfanar da wasu daga cikinsu a kotu, inda aka tura su gidan ajiya da gyaran hali.

Sai dai a nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar kasuwar, Aliyu Abubakar Umar, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa ana kan shirin tsara zaɓen sabbin shugabannin kasuwar.

Ya ƙara da cewa babu wani ɗan kasuwa da ake cin zarafinsa, tare da jaddada cewa jami’an tsaro ne suka kama wasu matasan kuma aka gurfanar da su a kotu, inda aka yanke musu hukunci bisa abin da suka aikata.

Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin wasu ’yan kasuwar da shugabancin kasuwar kan batun shugabanci da gudanar da zaɓe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button