Labarai

Sojin Sama Sun Kashe Manyan ’Yan Ta’adda a Harin Dajin Sambisa

Dakarun sojin saman kasarnan sun kashe wasu manyan ’yan ta’adda tare da lalata muhimman wurarensu a wani hari ta sama da suka kai a dajin Sambisa.

Harin, wanda aka kai a yankin Yuwe ƙarƙashin shirin Operation HADIN KAI, ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri da suka gano maboyar shugabannin ’yan ta’addan da kuma rumbunan ajiyar kayayyakinsu.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar sojin saman, Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Litinin 2 ga Maris 2026 a Abuja, ya bayyana cewa an gudanar da harin cikin tsari da kuma bin sahihan bayanan sirri.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan tantance sakamakon harin, an tabbatar da kashe wasu manyan kwamandoji da mayaka, tare da lalata kayayyakin da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.

Rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da kai hare-hare kan maboyar ’yan ta’adda domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Gabas.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button