Dakarun JTF Sun Ƙwato Dabbobi 257 Bayan Daƙile Harin ɓarayin Shanu a Gwarzo

Dakarun haɗin gwiwa na JTF ƙarƙashin jagorancin sojojin Rundunar 3 Brigade sun yi nasarar ƙwato dabbobi 257 bayan da suka daƙile wani hari da ɓarayin shanu suka kai a Ƙaramar Hukumar Gwarzo.
Aikin, wanda ya gudana da sanyin safiyar Lahadi 1 ga Maris, 2026, ya biyo bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:57 na safe, inda dakarun suka hanzarta kai ɗauki zuwa wata hanya da ake zargin ’yan bindigar ke bi.
A cewar sanarwar da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar, dakarun sun yi wa ’yan bindigar kwanton ɓauna a ƙauyen Dayi bayan samun rahoton cewa sun sato dabbobi daga ƙauyen Mainika da ke cikin Gwarzo.
Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan bindigar sun buɗe wuta kan dakarun, amma daga bisani suka tsere zuwa Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, inda suka bar dukkan dabbobin da suka sace.
Dabbobin da aka ƙwato sun haɗa da shanu 135, tumaki 119, akuya guda ɗaya da jakuna biyu, wanda jimillarsu ta kai 257.




