Tinubu Ya Sake Nada Dr. Ahmed Abubakar Audi a Matsayin Shugaban NSCDC

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake naɗa Ahmed Abubakar Audi a matsayin Babban Kwamandan Hukumar Tsaro da Kariya ta Farar Hula ta Najeriya, Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), na wa’adin shekaru biyar.
Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ta ce sabon wa’adin ya fara aiki daga ranar Juma’a, 27 ga watan Fabrairu, 2026.
Dr. Audi ya fara rike mukamin ne a shekarar 2021 bayan tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya umarci Dr. Audi da ya sake fasalta hukumar domin ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, musamman a daidai lokacin da rundunar ‘yan sanda ke mayar da hankali kan kare al’umma daga barayin daji, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.
Dr. Audi, wanda aka haifa a ranar 30 ga Satumba, 1967 a garin Laminga da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Nasarawa, ya fara karatunsa a jihar kafin ya halarci Kwalejin Malamai ta Jengre a Jihar Filato, inda ya samu takardar shaidar Grade II a 1987.




