Ketare

Gwamnatin Iran Ta Tabbatar da Mutuwar Ayatollah Ali Khamenei Bayan Hare-Haren Amurka da Isra’ila

Gwamnatin Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban addini da siyasa na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, bayan ikirarin farko da Donald Trump ya yi cewa hare-haren da United States da Israel suka kai sun kashe shi.

A cikin sanarwar da kafar yada labarai ta Iran ta fitar, an bayyana cewa Khamenei, mai shekaru 86, ya rasu yayin da aka kai hari a ofishinsa a daren Asabar. Ba a fayyace cikakken yadda aka kashe shi ko waɗanda za su gaje mukaminsa ba.

Gwamnatin ta bayyana rasuwar a matsayin wani sabon babi a tarihin ƙasar.

Majalisar Ƙoli ta Tsaron ƙasar Iran ta ce mutuwar Khamenei za ta zama mafarin “ƙarin yaki da azzalumai,” tana mai zargin Amurka da Isra’ila da kai hare-haren.

Har ila yau, an bayar da sanarwar kwanaki 40 na zaman makoki da kwana bakwai na hutu domin jimamin jagoran.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button