Gidauniyar Marigayi Prof. Jibril Isah Ɗiso Ta Buɗe Sabon Masallaci da Islamiyya a Kano

Gidauniyar Prof. Jibril Isah Ɗiso Charity Foundation for Disable and Needy ta ƙaddamar da buɗe sabon Masallacin Kamsul Salawati tare da Makarantar Islamiyya a yankin Ɗanbare da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano State.
An buɗe masallacin da makarantar ne a yammacin ranar Asabar 28 ga watan Fabrairu, 2026, inda tarin al’umma daga sassa daban-daban suka halarci bikin ƙaddamarwar, wanda ya haɗa da samar da ruwan sha ga al’ummar yankin.
Gidauniyar wadda aka kafa domin tallafa wa marayu da masu buƙata ta musamman, ‘ya’yan marigayi Farfesa Jibril Isah Ɗiso ne ke kula da ita tun bayan rasuwarsa.
Daga cikinsu akwai Alhaji Isah Jibril Isah Ɗiso, shugaban Kano Property Agents Development Association (KPADA), wanda ke jagorantar harkokin gidauniyar.
Da take zantawa da manema labarai yayin taron, Dr. Fa’iza Jibril Isah Ɗiso ta bayyana cewa buɗe masallacin da makarantar Islamiyyar, tare da samar da ruwan sha, hadiyya ce ga mahaifinsu marigayi Farfesa Jibril Isah Ɗiso, inda aka yi masa addu’ar Allah ya kyautata makwancinsa.
Ta ƙara da cewa makarantar Islamiyyar za ta riƙa karɓar ɗalibai daga wurare daban-daban, tare da ba marayu ilimi kyauta matuƙar an tabbatar da maraicinsu, musamman waɗanda suka rasa iyaye gaba ɗaya.
Dr. Fa’iza ta kuma yi kira ga al’umma da su ƙara himma wajen gudanar da ayyukan alkhairi ga ‘yan uwansu da suka rasu, domin su ci gaba da samun lada a cikin kabarinsu.
Bikin ƙaddamarwar ya samu halartar jama’a da dama daga sassa daban-daban, inda aka bayyana jin daɗi da godiya kan wannan gagarumin aiki na alkhairi da gidauniyar ta gudanar.



