Labarai

Najeriya Ta Gargaɗi ’Yan Ƙasarta Mazauna Iran da Yankin Gulf Kan Tsanantar Rikici

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci ’yan ƙasarta mazauna Iran da sauran ƙasashen yankin Gulf da su kasance cikin shiri tare da sanya idanu sosai kan halin da ake ciki, bayan ɓarkewar rikici a yankin.

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan da United States tare da haɗin gwiwar Israel suka ƙaddamar da hare-hare a cikin Iran da safiyar yau.

 

Rahotanni sun nuna cewa Tehran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa cikin Isra’ila da kuma wasu sansanonin sojin Amurka a yankin Gulf.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar, ta shawarci ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen da abin ya shafa da su kula da kansu tare da bin waɗannan matakai:

Su kasance cikin shiri tare da sanya idanu kan abubuwan da ke faruwa.

Su taƙaita zirga-zirgar da ba ta da muhimmanci.

Su bi umarnin hukumomin ƙasashen da suke zaune.

Su rika bibiyar sahihan kafofin yaɗa labarai domin sanin halin da ake ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button