Labarai

Kotu ta bada belin Abubakar Malami

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da bayar da belin tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdulaziz Malami kan kuɗin naira miliyan 200.

Sai dai kotun ta umarce su da a tsare su a gidan yarin Kuje har sai sun cika dukkan sharuɗɗan belin da aka gindaya musu.

Mai shari’ar ta yanke hukuncin ne bayan sauraron hujjojin neman beli da lauyansu, Joseph Daudu, ya gabatar a gaban kotu.

Kotun ta tanadi cewa kowannensu dole ne ya gabatar da mutane biyu a matsayin masu tsaya musu, inda ɗaya daga cikin masu tsayawar dole ne ya mallaki fili a unguwar Maitama ko Asokoro a Abuja.

Haka kuma, wajibi ne a ajiye takardun mallakar filin tare da fasfo na masu tsayawa a ofishin Mataimakin Magatakardan kotu.

Bugu da ƙari, kotun ta umarci Malami da ɗansa da su miƙa fasfonsu da hotunansu ga kotu a matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan belin.

An sanya ranar 4 ga Maris domin fara sauraron shari’ar.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ce ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin tallafawa ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button