Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Fara aiwatar da Mataki Na Farko Na Shirin Dakile Cutar Zazzabin Tsuntsaye

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da fara aiwatar da mataki na farko na shirin dakile cutar Zazzabin Tsuntsaye (Avian Influenza), bayan amincewar Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.

Sanarwar ta fito ne daga Kano State Ministry of Livestock Development, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar, Dakta Aliyu Isah Aliyu, wanda ya ce shirin zai mayar da hankali kan kariya, gano cutar da wuri, ƙarfafa matakan tsaro (biosecurity), da kuma gaggauta ɗaukar matakin da ya dace idan an samu ɓullar cutar.

Cutar Zazzabin Tsuntsaye wadda aka fi sani da Bird Flu, cuta ce mai saurin yaɗuwa a tsakanin kaji da sauran tsuntsaye, wadda kan haddasa mace-mace cikin gaggawa tare da janyo asarar tattalin arziki mai yawa ga manoman kaji.

Ma’aikatar ta ce shirin na da burin kare manoman kaji, tabbatar da lafiyar al’umma, da kuma ƙarfafa wadatar abinci a Kano da ma Najeriya baki ɗaya, har ma da ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita.

Kwamishinan ya jaddada ƙudirin ma’aikatar na ɗaukar matakan rigakafi da sarrafa cututtuka yadda ya kamata domin kare masana’antar kiwo da bunƙasa ci gaban dabbobi mai ɗorewa a jihar.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa kafuwar Ma’aikatar Raya Kiwo ta Jihar Kano wata alama ce ta hangen nesa da jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen ƙarfafa harkar kiwo da kuma dakile cututtuka da ka iya shafar rayuwar manoma a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button