Babban jami’n Gwamnatin Jihar ya naimi afuwar Dan jaridar da yaciwa mutuncin

Babban jami’in gwamnatin Kano State, SSR Auwalu Sani Rogo, ya bai wa dan jarida kuma mamba na Nigeria Union of Journalists (NUJ), Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai, hakuri kan cin mutuncin da aka yi masa a bainar jama’a.
Yabada hakurin ne a ranar Laraba a ofishin Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano, Abdullahi Ibrahim Waiya.
Taron sulhun ya samu halartar shugabannin Kano Online Media Chapel, karkashin jagorancin shugabanta, Comrade Abubakar Abdulƙadir Dangambo, da daraktocin ma’aikatar, tare da dan jarida kuma tsohon shugaban NUJ, Comrade Abdullahi Datti Arzai.
Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishina Waiya ya bukaci SSR da sauran jami’an gwamnati da su rika kyautata alaka da ’yan jarida domin ci gaban jihar.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da aiki kafada da kafada da kafafen yada labarai, yana mai amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
A nasa bangaren, Shugaban Kano Online Media Chapel, Comrade Abdulƙadir Dangambo, ya gode wa kwamishinan bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen warware matsalar.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da jan hankalin jami’an gwamnati da su fahimci rawar da ’yan jarida ke takawa a cikin al’umma.
Wannan yazone a gabar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ciki da wajen kasarnan sukayi Allah wadai da faruwar lamarin tare da bawa gwamnatin jihar Kano wa’adin sa’o’i 24 data dauki mataki ko suhadu agaban kuliya




