Labarai

Haryanzu El-Rufai yana tsare a hannun Hukumar ICPC

Lauyoyin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bayyana cewa har yanzu ba su samu wata amsa daga ICPC ba na buƙatar belinsa da suka gabatar, duk da cewa wa’adin awanni 48 na tsare mutum ba tare da tuhuma ba ya cika.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce lauyoyin sun nuna cewa har yanzu ba a gabatar musu da wata takardar umarnin kotu da ta ba da izinin ci gaba da tsare shi ba.

Sanarwar ta ce lamarin ya biyo bayan miƙa El-Rufai daga hannun EFCC zuwa ICPC a daren 18 ga Fabrairu, bayan ya kai kansa ofishin EFCC a safiyar 16 ga watan domin amsa gayyatar da aka yi masa.

A makon nan ne ake sa ran kotu za ta saurari wasu ƙararraki biyu da suka shafi lamarin. Daya daga ciki ita ce ƙarar take haƙƙin ɗan Adam da ya shigar kan Gwamnatin Tarayya da hukumomin bincike ciki har da ICPC, wadda za a saurara a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ranar 25 ga Fabrairu.

A cikin ƙarar, El-Rufai na neman kotu ta umarci a sake shi bisa beli, yana mai cewa tsare shi ba tare da cika sharuɗɗan doka ba ya saɓa haƙƙoƙinsa a matsayin ɗan Adam.

Ana kuma sa ran a rana guda za a gurfanar da shi kan tuhume-tuhumen da DSS ta riga ta shigar.

Lauyoyinsa sun jaddada cewa rashin amsa buƙatar belin da kuma rashin nuna takardar umarnin tsarewa na daga cikin abubuwan da suke ƙalubalanta a gaban kotu, yayin da suke jiran hukuncin shari’a kan buƙatunsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button