Labarai

Tattalin Arzikin Najeriya Cikin Hadari: Ma’aikatu Sun Koka Kan Rashin Karɓar Kasafin Kuɗi na 2025

Abuja, Najeriya – Tattalin arzikin Najeriya na fuskantar wani mummunan ƙalubale, yayin da rahotanni ke nuna cewa wasu manyan ma’aikatun gwamnati ba su karɓi ko kwabo ba daga cikin kasafin kuɗi na shekarar 2025, duk da amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

 

Wannan lamari ya haifar da damuwa a tsakanin ‘yan majalisa da masana tattalin arziki, inda suke ganin hakan na iya shafar ci gaban ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, ma’aikatu irin su Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida (Ministry of Interior) da Ma’aikatar Wutar Lantarki (Ministry of Power) sun bayyana cewa ba su samu ko sisi ba daga cikin kuɗaɗen ayyukan ci gaba (capital projects) na kasafin kuɗi na 2025.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa ma’aikatarsa ba ta samu ko kwabo ba a shekarar 2024 da kuma 2025, lamarin da ke nuna cewa shekaru biyu cif ba a yi musu kasafin kuɗi ba

Haka kuma, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan majalisa cewa ma’aikatarsa ta gudanar da ayyukanta ba tare da kasafin kuɗi na ci gaba ba a shekarar 2025

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button