Wasu Matasa Sun Yi Zanga-Zangar Lumana Kan Zargin Kai Hare-Hare Ga ’Yan Arewa

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da adalci ga kowane dan kasa ba tare da la’akari da yankinsa ba.
A cewar masu zanga-zangar, yayin da ’yan Kudu ke gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali a jihohin Arewa ba tare da tsangwama ba, akwai rahotannin da ke nuna cewa ana kai hare-hare kan wasu ’yan Arewa a wasu sassan Kudancin kasar.
Sun jaddada cewa Najeriya kasa ce ta kowa da kowa, inda babu wani dan kasa da ya fi wani.
A cewarsu, idan wata kungiya ta ji ana muzanta ta ko kuma ba ta cikin aminci, hakan na iya zama barazana ga hadin kan kasa baki daya.
Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace domin dakile duk wani rikici tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar kasar.




