Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wadanda ake zargi da satar motoci

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaki da satar ababen hawa, bayan kama wata ƙungiyar mutane shida da ake zargi da satar motoci tare da ƙwato motoci uku da aka sace.

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, kamen ya biyo bayan umarnin Kayode Adeolu Egbetokun na ƙarfafa ayyukan bincike da amfani da fasaha wajen yaki da aikata laifuka.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta musamman ta Special Intervention Squad (SIS), ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, ta kama Aliyu Mamman mai shekaru 35 a unguwar Hotoro Ring Road a ranar 13 ga Fabrairu, 2026. Ana zarginsa da kasancewa gogaggen mai satar mota.

Wanda ake zargin, mazaunin ƙaramar hukumar Gusau a Jihar Zamfara, ya amsa laifin satar motoci a jihohin Kano, Kaduna da Katsina.

 

Haka kuma ya fallasa sauran mambobin ƙungiyar da suka haɗa da Abdulhamid Usman, Saliha Abdulhamid, Auwal Shuaibu, Sani Bala da Ahmad Mannir, waɗanda tuni aka kama su.

Bincike ya kai ga ƙwato motoci uku da suka haɗa da Golf Wagon, Golf Opel da Hijet (Kurkura).

Kwamishinan ’Yan Sandan ya yaba wa jami’an rundunar ta musamman bisa ƙwazo da ƙwarewa wajen kama waɗanda ake zargi da kuma ƙwato motocin.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa na rundunar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button