Labarai

KCSEDA Ta Bukaci CP Ibrahim Adamu Bakori Ya Zurfafa Bincike Kan Harbin Matasan Kabara

Ƙungiyar Haɗin Kan Unguwar Kabara don Ilimi, Tsaro da Ci gaban Al’umma (KCSEDA) ta shigar da ƙorafi a rubuce ga Ibrahim Adamu Bakori, Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, kan buƙatar a zurfafa bincike game da harbin wasu matasa huɗu a unguwar Kabara, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar ɗaya daga cikinsu.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Haruna Salisu Sa’adu, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da Dala FM Kano a ranar Lahadi 22 ga watan Fabrairu, 2026, a Kano.

A cewarsa, ƙungiyar ta KCSEDA ta haɗa kai da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network domin mika ƙorafin ga ofishin Kwamishinan ƴan sanda, tare da buƙatar a gudanar da cikakken bincike kan lamarin da kuma ɗaukar matakin da ya dace domin kauce wa maimaituwar hakan a gaba.

Ya bayyana cewa, a kwanakin baya wasu jami’an tsaro sun je yankin Kabara domin kwantar da tarzoma sakamakon shigowar wasu ɓata-gari.

Sai dai a yayin aikin, jami’an sun saki wuta kan wasu matasa ‘yan unguwar da ba su da alaƙa da tarzomar, inda harbin ya rutsa da su huɗu, kuma ɗaya daga cikinsu ya rasu.

Haruna Salisu ya yi kira ga Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano da Gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta shiga lamarin domin tabbatar da adalci da kuma kare haƙƙin matasan yankin.

A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Global Community for Human Rights Network a Najeriya, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ya ce ƙungiyarsu ba za ta zuba ido haƙƙin matasan ya salwanta ba. Ya jaddada cewa za su ci gaba da bibiyar lamarin tare da KCSEDA har sai an gudanar da bincike mai zurfi kuma an ɗauki mataki a kan duk jami’in da aka samu da hannu a harbin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button